Mai Girma Ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani na tarayyar Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami, FNCS, FBCS, FIIM, MCPN. A ranar Laraba ya karbi bakuncin mahukuntan jaridar Muslim News Nigeria karkashin jagorancin mawallafinta Rasheed Abubakar a ofishinsa da ke Abuja.
Jaridar Muslim News Nigeria, itace Jaridar Musulunci mafi karfi a Najeriya, jarida ce da take ciki babu dare babu rana 24/7 a a Kafafen Sadarwa tana kuma wallafa rubututtukan ta wata-wata an kafa wannan gidan Jarida ne don ba da kulawa ta musamman ta kafofin watsa labarai ga al’ummomin musulmi da kawar da abubuwan da ba su dace ba (ga Musulmai) a kafofin watsa labarai na yau da kullun.
Daga cikin makasudan ayukkanya akwai taya murna ga irin nasarar da musulmi, wadanda suka yi fice a bangarori daban-daban, domin saka al’ummar musulmi alfahari, a Nijeriya da ma duniya baki daya.
A yayin fitar da gwarzo da sukayi karo na uku wato #MNAward2020 wanda Rawshield PR Media ta shirya, mawallafan Muslim News, sun zabi Mai Girma Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin fasahar zamani na tarayyar Najeriya ya zama gwarzon Musulmin Najeriya na shekarar, yayin da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya lashe kyautar a duniya.
“Wannan wata dama ce da muke bugun gaba da ita a shafinmu na Muslim News ta muke gabatar da lambar yabo ta gwarzon Musulmi na Najeriya na shekarar 2020, wanda mai Girma Ministan ya lashe, in ji Mr Abubakar, wanda ya yaba wa Ministan bisa yadda ya gabatar da jawabin bude taro a matsayin babban bako mai jawabi a Videon zamani (Virtual). a wajen taron karramawa/MN karo na 3 da aka gudanar a kwanan nan a Legas.
A cewar Abubakar, “Ganin baka samu damar halarta taron ba yasa muka, yanke shawarar lallai zamu samu lokacin da ya dace don gabatar muka da lambar yabo a gaban ka sai a yau Laraba, 3 ga Nuwamba, 2021 muka samu damar hakan.
Ministan wanda masoyansa suka fi sani da Sheikh Pantami ya kuma karbi Gwarzon Minista na 2020 daga Mawallafi, fitaccen dan jarida kuma marubucin “Islam and Media Series 1-4.
Yallabai, za ka iya tunawa, a shekarar da ta gabata, bayan nazari na tsanaki da nazari kan kokarin Ministocin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020, ka zama Ministan da yafi kowa kokari a cikin Ministocin Shugaba Muhammadu Buhari.
Wadannan nasarorin da ba a taba samun irinsu ba a tarihin wannan ma’aikatar, kuma daga cikin binciken da muka yi, mun samu cewa an samesu be ta hanyar aiwatar da Ayyukan Tattalin Arzikin fasahar zamani domin zamantar da Najeriya da warware wasu abubuwa muhimmai da ake bukata sama da shekaru goma.
“Za mu ba ka wannan lambar yabo a yau, ba wai kawai saboda kawa ba ce, ah ah sai don zaburar da wadanda suke rike da wasu madafun iko su kara kaimi, a matsayinka na ministan sadarwa da tattalin arzikin fasahar zamani na tarayyar Najeriya, ka zama wakili ga al’ummar Musulmi, al’umma na alfahari da kai da sauran duk al’ummar Musulmi da suke yi wa Musulunci abun kwarai, na gode kuma Allah Ya saka muka da alheri,” inji Abubakar.
Ministan ya yaba da karramawar da aka yi masa, inda ya ce: “A lokacin bikin karramawar, na shagaltu sosai, amma duk da haka na yi kokarin ganin na halrci taron a Videon zamani (virtual), nayi kokarin halarta ne domin na karfafa muna gwuwa. Na yi farin cikin halarta na, na kuma yi farin ciki da bukukuwan murnar nasarar da musulmi suka samu, kuma na yi farin ciki da duk abin da ya faru a wajen wannan taron.”
Farfesa Pantami ya yabawa mahukuntan gidan jaridar kan yadda suka tsaya tsayin daka, inda ya kara da cewa, “ku da kungiyar ku kuna aiki sosai, musamman wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jaridar, domin ba abu ne mai sauki a ci-gaba da rike irin wannan jarida ta Musulunci ba, musamman ma a kasa kamar Najeriya, inda ake da kyamar Musulunci, na san ba abu ne mai sauki ba, amma ka yi kokarin ka ci gaba da dawwama kamar yadda ka kasance na tsawon shekaru.”
A cewarsa, “Ba zan iya tunawa da wata jaridar da ta fito daga cikin al’ummarmu wacce ta yi tsayin daka irin taku ba, kalubale ne babu makawa, su ne ginshikin samun nasara a rayuwa, kai da kungiyar ku za ku gamu da kalubale da dama, musamman ma idan ana maganar samun, tallafi da sauran su, haka rayuwa take gaba daya.
“Idan kun tsaya tsayin daka da gaskiya, Allah zai tainakeku, ya kuma sa ku samu nasarori sosai, lokaci ne zai kaimu zaku zama wani babban abu a Najeriya da ma waje, Musulmin duniya za su yi alfahari da ku.
“Ni ma nakan karanta wasu labarai, ba na yawan bibiyar labarai, amma idan ana maganar Labaran Musulunci nakan yi kokarin bibiyarsa, a gaskiya ma wani lokaci ina daukar tsawon wata guda bana online ba tare da karanta Labarai ba, amma idan na dawo online nakayi kokoarin bibiyar labarun jaridar Muslims News (MN) na karanta kuma nayi Sharing. Allah Ta’ala ya saka muku da mafificin alheri.
By Munir Assalafiy